Ƙungiyar masu gidajen rediyo da talabijin sun yi barazanar kauracewa tarukan Wike

Ƙungiyar masu gidajen rediyo da talabijin masu zaman kansu ta Najeriya (IBAN) ta buƙaci ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, da ya janye kalaman da ya yi kan ɗan jarida Seun Okinbaloye tare da ba shi haƙuri a bainar jama’a kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
IBAN ta kuma yi barazanar kauracewa duk wani taron manema labarai da Wike zai shirya idan bai cika wannan buƙata ba.
Wannan na zuwa ne bayan Wike ya ce zai iya “harbe” Okinbaloye yayin da yake sukar ra’ayinsa a wani shirin talabijin, kafin daga bisani ya ce ba ya nufin hakan a zahiri.
Ƙungiyar ta ce duk da bayanin da aka bayar daga baya, irin wannan magana ba ta dace da jami’in gwamnati ba, domin na iya tsoratar da ‘yan jarida da kuma ƙara tsananta yanayin aikinsu.
IBAN ta buƙaci ministan ya janye maganarsa, ya ba da haƙuri, sannan ya nuna goyon bayansa ga ‘yancin aikin jarida, tana mai gargaɗin cewa rashin yin hakan zai sa su dakatar da yada labaran duk ayyukansa.




