Hisbah Ta Kama Shugaban Ƙaramar Hukuma a Otal da Ƙananan Yara a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani shugaban ƙaramar hukuma bisa zargin kasancewa a ɗakin otal tare da wasu ƙananan yara, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an Hisbah sun gudanar da samamen ne a wani otal da ke cikin birnin Kano, inda suka tarar da mutumin a cikin ɗaki tare da yaran da ake zargin ƙanana ne.
Majiyoyi sun bayyana cewa kamen ya biyo bayan bayanan sirri da hukumar ta samu, wanda ya sa ta dauki matakin gaggawa domin dakile abin da ake zargin ya saba wa doka da kuma dokokin addini.
Sai dai har yanzu hukumar Hisbah ba ta fitar da cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru ba, ko kuma ainihin shekarun yaran da aka samu a wurin.
Wani jami’i daga hukumar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ana ci gaba da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru, tare da tabbatar da adalci ga kowa.
A halin yanzu, ana jiran karin bayani daga hukumomi kan ci gaban bincike da kuma matakan da za a dauka dangane da lamarin.
Apn hausa




