Labarai

‘Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin Garkuwa da Mutane a Hanyar Nasarawa Eggon–Akwanga, Sun Kashe Ɗaya Daga Cikin Masu Laifin

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, lokacin da jami’an ‘yan sanda na ofishin Nasarawa Eggon ke gudanar da sintiri na yau da kullum a kan hanyar Nasarawa Eggon zuwa Akwanga.

 

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an sun ci karo da wata alama ta shirin aikata laifi a kusa da wani wurin nika shinkafa (Rice Mill), inda wasu matasa dauke da makamai suka toshe hanya da duwatsu domin kai hari ga masu ababen hawa.

 

Da ganin zuwan jami’an ‘yan sanda, wadanda ake zargin sun bude musu wuta, lamarin da ya janyo mayar da martani cikin gaggawa daga jami’an tsaro.

 

A sakamakon artabun, an kashe daya daga cikin wadanda ake zargin, yayin da sauran suka tsere zuwa cikin daji dauke da raunukan harbi.

 

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ramhan Nansel, ya fitar, ya bayyana cewa an gano gawar wanda aka kashe din mai suna Auta Habu, mazaunin wani rugar Fulani a Gidan Waya, karamar hukumar Nasarawa Eggon.

 

Sanarwar ta kara da cewa bincike ya nuna marigayin yana da hannu a wasu munanan laifuka da dama a yankin.

 

Bugu da kari, rundunar ta tabbatar da cewa an kwashe duwatsun da aka toshe hanyar da su, kuma a yanzu hanyar ta zama lafiya ga matafiya da sauran masu amfani da ita.

 

Rundunar ‘yan sandan ta kuma bayyana cewa tana ci gaba da farautar sauran wadanda suka tsere domin cafke su tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

 

A karshe, rundunar ta bukaci al’umma da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani motsi mai kama da shakku ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro a yankunansu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button