Kotun Jiha Ta Soke Nasarar Basaf, Ta Tabbatar da Ali Musa Ɗanmaliki a Matsayin Shugaban Karamar Kumbotso

Babbar Kotun Jiha mai lamba 17 da ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Abdu Mai Wada Abubakar ta soke nasarar Abdullahi Basaf a matsayin shugaban karamar hukumar Kumbotso da ke jihar Kano.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Talata, 24 ga watan Maris, 2026, bayan shafe lokaci ana sauraron karar da aka shigar gabanta kan sahihancin zaben shugabancin karamar hukumar.
A hukuncin da ta zartar, kotun ta tabbatar da Ali Musa Ɗanmaliki, wanda aka fi sani da “Hardworker”, a matsayin halastaccen shugaban karamar hukumar Kumbotso.
Haka kuma, kotun ta bayyana cewa takardar shaidar cin zabe da Hukumar Zabe ta Jihar Kano (KANSIEC) ta bai wa Abdullahi Basaf ba ta da inganci, inda ta ayyana ta a matsayin haramtacciya.
Bugu da kari, kotun ta umarci hukumar KANSIEC, wadda ita ce wanda ake kara na uku a shari’ar, da ta gaggauta bai wa Ali Musa Ɗanmaliki takardar shaidar cin zabe ba tare da bata lokaci ba.
Har ila yau, kotun ta jaddada cewa wajibi ne gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da aiwatar da wannan hukunci cikin gaggawa, domin mutunta doka da oda.




