Labarai

’Yan bindiga sun sace Sakataren mulki na Karamar Hukumar Kibiya Hon. Hamza Durba

Arewa Updates ta rawaito cewa, Babban Jamiʼin Harkokin Tsaro na Karamar Hukumar Kibiya Malam Musa Hussaini Ibrahim ya tabbatar wa da Arewa Updates faruwar lamarin.

 

Ya ce, maharan su 6 a kan babura ɗauke da bindigu sun shiga gidansa da ke garin Dinya a mazabar Durba inda suka yi awon gaba da shi.

 

A cewarsa, sun tarar da iyalansa a gidan amma ba su ɗauki kowa ba, kuma ba su yi ko harbi ba, sai suka sa shi a gaba suka tafi da shi.

 

Bayan faruwar lamarin tuni hukumomin tsaro suka shiga bincike da bin sahu don ceto shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button