Ɓatagari Sun Kai Hari Kan Hadimin Gwamnan Kano, Sun Sassare Shi

Wasu ɓatagari sun kai mummunan hari kan Mai Taimakawa Gwamnan Jihar Kano kan harkokin yaɗa labarai, Hon. Gamboliya Jaʼen, inda suka sassare shi a sassa daban-daban na jikinsa.
Gamboliya Jaʼen ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a unguwar Jaʼen, bayan gidan Katakore kusa da Big Trust, a lokacin da yake dawowa daga sayen kayan Sallah ga yara.
A cewarsa, maharan sun afka masa ba zato ba tsammani, inda suka rika sara ta ko ina a jikinsa, lamarin da ya sa daga bisani bai ƙara sanin abin da ya faru ba.
Bayan aukuwar lamarin, an garzaya da shi zuwa Asibitin Murtala domin samun kulawar likitoci, yayin da Gwamnan Jihar Kano ya shiga cikin lamarin domin tabbatar da an ba shi kulawar da ta dace.
Haka kuma, ya yaba da ƙoƙarin da jami’an ‘yan sanda na yankin Sharaɗa suka yi wajen daukar matakai kan lamarin.
Gamboliya Jaʼen ya ce ya bar komai ga Allah, yana mai cewa duk wanda ke son ganin bayansa, Allah Ya nuna cewa yana raye.
A wani bangare kuma, an tuna cewa a watan Agustan 2025, wasu ɓatagari sun kashe Babban Mai ɗauko wa Gwamnan Kano rahoto a Ma’aikatar Tarihi da Al’adu ta jihar, Hon. Sadiq Gentle, a wani hari makamancin wannan.




