Ketare

Saudiyya Ta Bukaci Musulmi Su Fita Duba Jinjirin Watan Shawwal gobe

Mahukuntan ƙasar Saudi Arabia sun bukaci dukkan Musulmi da ke faɗin ƙasar da su fita domin duba jinjirin watan Shawwal a yammacin ranar Laraba, 29 ga watan Ramadan na shekarar 1447 Hijira.

A sanarwar da aka fitar, an bayyana cewa ranar ta yi daidai da 18 ga Maris, 2026, kuma ana kira ga duk wanda ya ga jinjirin watan da idonsa ko ta amfani da na’urar hangen nesa (binoculars) da ya gaggauta sanar da kwamitin duban wata mafi kusa da shi domin yin rajistar shaidarsa.

Mahukuntan sun jaddada cewa wannan mataki na daga cikin tsarin tabbatar da ganin watan Shawwal wanda ke nuna karshen watan Ramadan da kuma fara bukukuwan Eid al-Fitr.

 

Masu ruwa da tsaki sun kuma bukaci al’umma su hada kai wajen gudanar da wannan aiki cikin gaskiya da amana domin tabbatar da sahihancin sanar da ranar Sallah.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button