Ketare

Najeriya Ta Zo Ta 39 a Ƙarfin Soji a Duniya

 

Wani rahoto da Ƙungiyar Global Firepower Index, wadda ke fitar da jadawalin ƙarfin sojojin ƙasashen duniya, ya nuna cewa Najeriya ta zo matsayi na 39 a jerin ƙasashe 145 na duniya wajen ƙarfin soji a shekarar 2026, tare da zama ta uku mafi ƙarfi a nahiyar Afirka.

Rahoton ya bayyana cewa Najeriya ta zama ƙasar da ke ba da gudummawa mafi girma wajen tabbatar da tsaro a yankin Yammacin Afirka, sakamakon kasafin kuɗin da take warewa bangaren tsaro da kuma ci gaba da sabunta makaman yaƙi da kayan aiki na sojoji.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa dakarun sojin Najeriya na taka muhimmiyar rawa wajen murƙushe ayyukan ta’addanci, musamman a yankin Arewa maso Gabas, inda suke ci gaba da fafatawa da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.

Baya ga hakan, rahoton ya nuna cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen gaba-gaba a Afirka wajen wanzar da zaman lafiya, ta hanyar tura sojoji da jami’an tsaro zuwa ƙasashen nahiyar da ke fuskantar rikice-rikice domin dawo da doka da oda.

Masana harkokin tsaro na ganin wannan matsayi a matsayin wata shaida ta ƙoƙarin da Najeriya ke yi wajen ƙarfafa rundunonin tsaronta da kuma rawar da take takawa a fagen tsaro na yanki da na duniya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button