Labarai

Dalibai 36 Sun Sauke Alƙur’ani a ANNUR Academy

An gudanar da gagarumar saukar Alƙur’ani Mai Girma a Makarantar Mustapha Dangi ANNUR Memorial Academy da ke Limawa, Hotoro, a Ƙaramar Hukumar Tarauni.

Taron ya gudana cikin tsari, inda malamai, iyaye, da baƙi suka hallara domin shaida wannan babban ci gaba na ilimi da tarbiyya. Wannan saukar ta nuna ƙoƙarin makarantar wajen gina ɗalibai masu nagartar ilimin addini da kyawawan ɗabi’u.

Wannan shi ne karo na uku da makarantar ke gudanar da saukar Alƙur’ani, inda aka yaye ɗalibai 36 da suka kammala karatun littafin Allah cikin nasara.

Hakan ya nuna jajircewar ɗaliban tare da kulawa da sadaukarwar malamansu.

Mahalarta taron sun bayyana farin cikinsu, suna mai yaba wa makarantar bisa irin rawar da take takawa wajen bunƙasa ilimin addini a tsakanin yara.

Daga cikin waɗanda suka samu wannan nasara akwai Aisha Garba Ubale Damnatta, ‘yar gidan Janar Manaja na Radio Nigeria Pyramid FM, Dr. Garba Ubale Dambatta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button