Musulman Lagos Sun Fitar da Matsaya Kan Zaɓen Gwamna na 2027

Kungiyar al’ummar Musulmi ta Jihar Lagos, wato Muslim Community of Lagos State (MCLS), ta bayyana aniyarta ta janye goyon baya ga duk wata jam’iyyar siyasa da ba ta tsayar da ɗan takarar gwamna Musulmi ba a zaɓen gwamnan jihar Lagos na shekarar 2027.
Kungiyar ta bayyana wannan matsaya ne a madadin Musulman Jihar Lagos yayin babban taron ta na shekara-shekara da aka gudanar a Masallacin Sakatariyar kungiyar da ke Alausa, a jihar Lagos.
A yayin taron, mahalarta sun bayyana damuwarsu kan abin da suka kira keɓe Musulmai daga muhimman mukaman shugabanci, musamman a bangaren ilimi da sauran manyan mukaman gwamnati.
Kungiyar ta bukaci Gwamnatin Jihar Lagos da ta dauki ƙarin malamai na harshen Larabci da Ilimin Addinin Musulunci (Islamiyya) a makarantun gwamnati, tare da tabbatar da adalci da daidaiton addini wajen nada shugabanni a matakai daban-daban na gwamnati.
A cewar MCLS, an dauki wannan mataki ne sakamakon rashin isasshen wakilcin Musulmai a manyan mukaman siyasa da na gwamnati a jihar Lagos, duk da cewa Musulmai na daga cikin mafi rinjayen al’ummar jihar.
Kungiyar ta kuma jaddada cewa tsawon shekaru 12 ana mulkin Jihar Lagos karkashin gwamnonin Kirista, ciki har da gwamnan da ke kan mulki a halin yanzu, lamarin da kungiyar ke ganin ya dace a sauya domin a samu daidaito, adalci da wakilci ga dukkan bangarorin al’umma.
MCLS ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da su mutunta muradin al’ummar Musulmi, tare da gargadin cewa duk jam’iyyar da ta bijire wa wannan bukata, za ta rasa kuri’un Musulmai a zaɓen gwamna na shekarar 2027.
Haka kuma, kungiyar ta bukaci Musulmai da su ƙara shiga harkokin siyasa, su tabbatar sun yi rijistar katin zaɓe, sannan su fito kwansu da kwarkwatarsu wajen mara wa ‘yan takarar Musulmi baya.



