Siyasa
Ganduje da Alhassan Ado Doguwa sun goyi bayan Murtala Sule Garo ya zama mataimakin gwamnan Kano

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje, da tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa, tare da wasu manyan ‘yan siyasa sun goyi bayan Murtala Sule Garo ya zama mataimakin gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Doguwa ya fitar, inda yace an cimma matsayar ne bayan tattaunawa tsakanin jagorori da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.



