Rundunar ‘Yan Sandan Ondo Ta Kama Mutane Biyu Kan Zargin Garkuwa da Mutane

Waɗanda aka kama sun haɗa da Abubakar mai shekaru 25 da Oliver Okoh mai shekaru 35.
An cafke su ne a yankunan titin Sabo Sango da Ilado bayan wani samame na musamman da sashen yaƙi da garkuwa da mutane ya gudanar bisa sahihan bayanan sirri.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Jimoh Abayomi, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar a Akure, babban birnin jihar.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin na cikin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane.
A cewarsa, mutanen sun fara bayar da muhimman bayanai ga masu bincike, yayin da aka kwato wasu babura da kayan da ake zargin ana amfani da su wajen aikata laifukan.
Lamarin ya biyo bayan sace wasu ma’aurata a yankin Olaribigba Estate da ke Ilu Abo, inda maharan suka yi musu kwanton bauna a kan hanyarsu ta komawa gida.
A halin yanzu, mazauna yankin Akure sun nuna damuwa kan karuwar rashin tsaro, tare da kira ga hukumomi da su ƙara kaimi wajen dakile ayyukan ta’addanci da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.




