Labarai

’Yan Sanda Sun Kama Mutane 6 Kan Damfara Ta Hanyar Sadarwa, Sun Kwato Kwamfutoci 400 da Wayoyi 1,000

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta samu babbar nasara a yaƙin da take yi da laifukan yanar gizo, bayan da ta cafke mutane shida da ake zargi da shirya babbar damfara ta hanyar sadarwa wadda ta janyo asarar kuɗi sama da Naira biliyan 7.7.

 

Rahoton da rundunar ta fitar ya bayyana cewa, Cibiyar Yaƙi da Laifukan Yanar Gizo ta Ƙas ce ta tono wannan makirci, inda ake zargin ƙungiyar da satar airtime da bayanan intanet na wani kamfanin sadarwa ta hanyar amfani da dabarun kwamfuta.

Binciken ’yan sanda ya nuna cewa an samu kutse cikin tsarin biyan kuɗi da lissafin kamfanin, bayan da aka sace bayanan shiga (login details) na wasu ma’aikata.

Wannan ya bai wa masu laifin damar shiga manyan tsarin kamfanin, inda suka rika karkatar da airtime da bayanan intanet cikin sirri na tsawon lokaci.

Bayan makonni na tattara bayanan sirri da sa ido, ’yan sanda sun kai samamen hadin gwiwa a jihohin Kano da Katsina, sannan aka kama wani daga cikin waɗanda ake zargin a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

A yayin samamen, ’yan sanda sun kwato kadarori masu yawa, ciki har da gidaje biyu a Kano, ƙananan gine-ginen kasuwanci (mini-plazas) guda biyu kwamfutoci, laptops sama da 400, wayoyin hannu kimanin 1,000, da motar Toyota RAV4 guda ɗaya.

Haka kuma, an gano kuɗaɗe masu yawa a asusun bankunan da ake danganta da waɗanda ake zargin.

 

Rundunar ’yan sandan ta tabbatar da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button