Labarai

Kwamishinan Matasa da Wasanni na Kano, Mustapha Rabiu Kwankwaso, Ya Ajiye Aiki

Mustapha Rabiu Kwankwaso, Kwamishinan Ma’aikatar Matasa da Ci gaban Wasanni ta Jihar Kano, ya sanar da murabus dinsa daga mukaminsa, tare da ficewa daga cikin Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano.

 

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kwankwaso ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne cikin zuciya mai cike da alhini, inda ya gode wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa damar da ya ba shi ta yi wa al’ummar jihar hidima.

 

Ya ce ya amfana ƙwarai da ƙwarewa da darussan da ya koya a lokacin da yake riƙe da muƙamin, tare da nuna godiya bisa amincewa da aka yi masa.

 

Mustapha Rabiu Kwankwaso ya kuma yi addu’ar cewa matasa a Jihar Kano za su ci gaba da samun kulawa da goyon baya da ya dace, yana mai fatan shirye-shiryen ci gaban wasanni da aka assasa za su ci gaba da bunƙasa a nan gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button