Labarai
Rundunar ‘Yansanda a Jihar Kaduna ta hana gudanar da taron da magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, suka shirya don bikin zagayowar ranar haihuwarsa a jihar.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ‘yansandan sun bayyana cewa za su kama duk wani mutum ko ƙungiya da ta ci gaba da shirya taron duk da umarnin haramta taron.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Mansir Hassan, ya ce bincike da rahotannin sirri sun nuna cewa “wasu miyagu na shirin fakewa da taron domin tayar da fitina da haddasa tashin hankali da kuma tayar da rikici a jihar.
Rundunar ta kuma bayyana cewa lokutan taron sun yi karo da zaɓen fidda gwani na wasu jam’iyyun siyasa da aka riga aka sanarwa ‘yansanda su kamar yadda dokokin Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) suka tanada




