Kwankwasiyya Ta Nuna Damuwarta Kan Gyaran Dokar Zaɓe

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar, Habibu Sale Mohammed, ya sanya wa hannu, wadda aka rabawa manema labarai a Kano.
A cewar ƙungiyar, matakin ya sake fito da barazanar da ke tattare da ƙaruwar rinjayen jam’iyya ɗaya a ɓangarorin zartarwa da majalisar dokoki.
Ta ce APC na da tasiri mai yawa a yanzu, musamman bayan sauya shekar wasu zaɓaɓɓun jami’ai daga jam’iyyun da suka tsaya takara a ƙarƙashinsu.
Kwankwasiyya ta bayyana cewa sauya shekar ba wai sauyin siyasa kawai ba ne, illa yana haifar da tambayoyi na ɗabi’a da na kundin tsarin mulki.
A cewarta, wakilan da aka zaɓa sun samu amana ne daga al’umma bisa wani tsari da manufa ta jam’iyya, don haka sauya sheƙa ba tare da cikakken bayani ko tuntubar mazaɓa ba na iya karkatar da wakilcin dimokuraɗiyya.
Sanarwar ta jaddada cewa dimokuraɗiyyar Najeriya an gina ta ne kan tsarin daidaito da juna (checks and balances), inda adawa mai ƙarfi da ‘yancin majalisa da sauraron ra’ayin jama’a ke zama ginshiƙai na tafiyar da mulki.
Ƙungiyar ta yi nuni da cewa muhawarar da ta biyo bayan gyaran Dokar Zaɓe misali ne da ke nuna yadda rinjaye a majalisa zai iya rage sa ido da ƙalubalantar shawarwarin gwamnati, duk da ra’ayin jama’a.




