Labarai
Gaskiyar abun da yafaru’ a Hukumar Civil Defence dake nan kano

Hukumar NSCDC reshen Jihar Kano ta kama ‘yan kasashen waje 20 a yankin Danbare da ke cikin karamar hukumar Kumbotso.
Kwamandan jihar, Mohammed Hassan-Agalama, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.
Ya ce an kama wadanda ake zargin, wadanda suka fito daga Sudan da Chadi da Kamaru da kuma Jamhuriyar Nijar, ne bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma gudanar da aiki na hadin gwiwa.
Hassan-Agalama ya ce binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin ba su iya gabatar da sahihan takardun tafiye-tafiye ko na shaidar zama ba, lamarin da ya janyo damuwa kan yadda suka shigo da kuma abin da su ke yi.
Ya kara da cewa kayayyakin da aka kwato sun hada da wayoyin Android guda 10.



