Kotu Ta Umurci Birtaniya Ta Biya Diyya Ga Iyalin Masu Haƙar Kwal da Aka Kashe a 1949

Wata kotu a Najeriya ta umurci gwamnatin Birtaniya da ta biya diyar kuɗi har fam miliyan 20 ga iyalai 21 na masu haƙar kwal da aka kashe a shekarar 1949 a kudu maso gabashin ƙasarnan zamanin mulkin mallaka.
A wancan lokaci, ƴan sandan mulkin mallaka, waɗanda suka haɗa da ƴan Najeriya da Turawa, sun harbe ma’aikatan haƙar kwal da ke tsaka da yajin aiki domin neman a inganta musu yanayin aiki, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 21 tare da jikkata wasu da dama.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya bayyana kisan a matsayin ɗaya daga cikin munanan ayyukan danniya da aka taɓa aikatawa a ƙarƙashin mulkin mallakar Birtaniya a ƙasar.
Masana tarihi sun ce wannan kisa ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙara ƙarfin fafutukar neman ƴancin kai, wadda daga bisani ta kai ga samun nasarar ƴancin Najeriya a shekarar 1960, shekaru 11 bayan faruwar lamarin.
Rahotanni sun nuna cewa iyalan waɗanda abin ya shafa tare da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam sun shafe shekaru masu yawa suna fafutukar ganin an amince da laifin da aka aikata tare da biyan diyya da ta dace.
BBC ta nemi jin ta bakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Birtaniya kan hukuncin kotun, amma zuwa lokacin haɗa wannan labari, ba a samu wata amsa daga gare ta ba.




