
Babban Mai Daukowa gwamna Rahoto a Ma’aikatar Ayyuka, Hon. Kamis Bako Ayagi, ya raba kayan makaranta ga yara sama da 400 a yankin Ayagi, a wani yunƙuri na tallafa wa fannin ilimi da ƙarfafa makomar yara masu tasowa.
An gudanar da taron rabon kayan ne a kofar gidan Sarkin Ayagi, inda jama’a da dama suka halarta, ciki har da iyaye, shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi.
Da yake jawabi a wajen taron, Hon. Kamis Bako ya bayyana cewa tallafin ya zo ne a daidai lokacin da yara ke buƙatar ƙarin tallafi domin samun ingantaccen ilimi.
Ya jaddada cewa zai ci gaba da tallafa wa harkar ilimi a yankin, kamar yadda Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya koyar da su a matsayin jagoranci mai mayar da hankali kan jin kan al’umma.
Hon. Kamis ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ƙoƙarin da yake yi na hidimtawa al’ummar Kano ba tare da nuna bambanci ba, yana mai cewa irin ayyukan da gwamnan ke aiwatarwa sun sanya ‘yan jihar cikin fata da bege na samun ci gaba mai ɗorewa.
“Idan muka duba irin ƙoƙarin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke yi na hidimtawa jama’a, babu abin da za mu ce face godiya.
A yau, shi ne ke bin ‘yan Kano bashi, ba mu ne ke binsa ba,” in ji Hon. Kamis Bako.
Wasu daga cikin iyaye da shugabannin al’umma sun nuna farin cikinsu da wannan tallafi, inda suka bayyana cewa rabon kayan makarantar zai rage musu nauyi tare da ƙarfafa yaran su maida hankali kan karatu.
Taron ya ƙare cikin farin ciki da addu’o’in alheri ga gwamnatin jihar Kano da masu tallafa wa ci gaban ilimi




