Gwamnatin taraya ta bayanna cewa za ta soma yi wa ɗaliban jami’o’in ƙasar nan gwajin miyagun ƙwayoyi a wani mataki na daƙile yaɗuwar ta’ammali da ƙwayoyin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, Ma’aikatar Ilimi ta kasa tare da haɗin gwiwar Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA ne za su jagoranci aikin.
Hakan na zuwa ne bayan ganawar Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya da kuma ministan ilimin ƙasar, Olatunji Alausa a ranar Laraba.
Ɓangarorin biyu sun kuma amince da ɓullo da daftarin koyar da darasin ilimin ta’ammali da ƙwayoyi a makarantun sakandiren ƙasar.
Buba Marwa wanda ya jagoranci tawagar jagororin hukumar NDLEA ya bayyana cewa gwajin ƙwayar zai shafi duk ɗaliban jami’o’in da sabbin da za su shiga.
Yayin da yake jawabi a wajen ganawar, Buba Marwa ya ce za su mayar da hankali ne kan makarantun ƙasarnan, waɗanda ya ce akwai miliyoyin yara da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ilimi ta ƙasa.




