Kotun Tarayya Ta Tsayar da 18 ga Yuni Don Ci Gaba da Shari’ar mawaki Rarara na zarginsa da aikata laifin satar fasaha

Ana sa ran fitaccen mawaki, Dauda Adamu Kahutu Rarara, zai gurfana a gaban Federal High Court da ke zamanta a Kano a ranar 18 ga watan Yuni domin ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi tsakaninsa da wani mawaki, Isa Ibrahim Zage.
Shari’ar wadda ke gaban Mai shari’a ML Shu’aibu ta samo asali ne daga zargin da Zage ya ke yi wa Rarara na satar fasaha, inda ya ce mawakin ya kwaikwayi wakarsa mai suna “Jirgin Ceto” da ya saki a ranar 12 ga Disamba, 2022, yayin da Rarara ya fitar da tasa a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
A zaman kotun na baya-bayan nan, an kammala sauraron shaidun masu ƙara, yayin da ake sa ran a fara sauraron shaidun wanda ake ƙara a zaman na gaba, inda ake tsammanin Rarara zai bayyana domin amsa tambayoyi.
Bayan zaman kotun, lauyan wanda ake ƙara, Barrister Abdulmunafi Ibrahim Ma’aji, ya yi karin bayani kan yadda shari’ar ta gudana, haka kuma lauyan mai ƙara, Barrister Muhammad Sulaiman Ahmad (Nazeer), ya bayyana nasa ra’ayi kan zaman.
Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Yuni domin ci gaba da shari’ar.


