Labarai
SANARWA DAGA HUKUMAR GUDANARWA – AHRASJO NEWS

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu,
Hukumar gudanarwa ta kafar yaɗa labarai ta Ahrasjo News na miƙa sakon godiya ta musamman ga ɗumbin masu bibiyar shafinmu bisa goyon baya da amincewar da kuke ci gaba da nuna mana.
Muna sanar da ku cewa, sakamakon wasu muhimman gyare-gyare da muke aiwatarwa domin ƙara inganta kwarewar ayyukan da muke gabatar muku, za a samu ɗan jinkiri na watsa shirye-shiryenmu na ɗan lokaci.
Da zarar mun kammala waɗannan gyare-gyare, za mu dawo gare ku da sabbin tsare-tsare masu kayatarwa da ingantattun shirye-shirye fiye da yadda kuka saba.
Sign by MD
Saeed Bin Usman.




