Labarai

Gwamnan Bauchi Ya Sallami Kwamishinan Tsaro da Harkokin Gida

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya sallami Kwamishinan Tsaro da Harkokin Gida, Alhaji Ibrahim Gambo Galadima, daga muƙaminsa nan take.

Matakin ya fito ne a cikin wata sanarwa da Mai Ba Gwamna Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar a safiyar ranar Litinin.

 

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya amince da yin ɗan gyara a majalisar zartarwar jihar, wanda ya haifar da cire Galadima daga mukaminsa.

 

A cewar sanarwar, matakin na daga cikin tsarin sake duba ayyukan kwamishinoni domin ƙarfafa tafiyar da mulki da kuma inganta ayyukan gwamnati a faɗin jihar.

 

Gwamna Bala Mohammed ya yaba wa Ibrahim Gambo Galadima bisa gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake rike da mukamin, tare da yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba.

 

Gwamnatin Jihar Bauchi ta kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen inganta tsaro, tabbatar da zaman lafiya, da samar da kyakkyawan shugabanci, inda ta ce za a sanar da wanda zai gaje shi a kan lokaci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button