Bijilanti Sun Kama Wanda Ake Zargi da Hada Kai da Mata Wajen Zubar da Ciki a Fagge

Kwamandan Bijilanti na Ƙaramar Hukumar Fagge, Tanimu Isma’il, ya sanar da kama wani mutum mai suna Sulaiman Lawan bisa zargin aikata laifuka da suka shafi zubar da ciki da kuma binne jarirai.
A cikin wani gajeren bidiyo da ya aike wa manema labarai a daren Laraba, Kwamandan ya ce an kama wanda ake zargin ne a Unguwar Sabon Birni, Mazabar Kwaciri da ke cikin Ƙaramar Hukumar Fagge, bayan samun sahihan rahotannin sirri a kansa.
Ya bayyana cewa ana zargin Sulaiman Lawan da kaurin suna wajen hada kai da wasu mata domin zubar musu da ciki, tare da kuma zuwa binne jariran da aka haifa a bayan gari.
Kwamandan ya ƙara da cewa suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin da kuma zakulo duk wasu da ka iya hannu a ciki.
Hukumar ta kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar kai rahotannin sirri domin dakile irin waɗannan laifuka a cikin al’umma.



