Majalisar gudanarwa ta Bayero University Kano, ta naɗa Farfesa Haruna Musa, a matsayin shugaban jami’ar na 12.

Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Bayero, Kano, ta amince da nada Farfesa Haruna Musa, fsi, a matsayin Shugaban Jami’a (Vice-Chancellor) na 12 na jami’ar. Wannan nadin yana da cikakken wa’adin shekara biyar (5) kacal, daga ranar 18 ga Agusta, 2025.
A cikin wata wasika da Pro-Chancellor kuma Shugaban Majalisar Gudanarwa, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya rattaba wa hannu, an bayyana cewa an yanke wannan hukunci ne bisa doka ta Sashe na 4 na Dokar Gyaran Harkokin Jami’o’i (Universities Miscellaneous Provisions Amendment Act) ta shekarar 2003. An bayyana cewa Majalisar ta yanke wannan hukunci ne a zaman ta da aka gudanar a ranar Alhamis, 3 ga Yuli, 2025, bayan nazari da la’akari da shawarwarin Kwamitin Zaɓe.
Dr. Gawuna ya taya Farfesa Haruna Musa murna tare da yi masa fatan samun nasara da tasiri mai kyau a lokacin aikinsa.




