Labarai

Siyasa ko naiman suna Malamin Firamare Ya Baiwa Gwamnan Kano Kyautar Dubu talatin

Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano Ibrahim Abdullahi Waiya, shine ya gabatar wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kyautar da wani malamin firamare ya bayar, a zaman Majalisar Zartarwar Jihar.

Waiya ya bayyana cewa malamin mai suna Abubakar Musa ne ya bayar da kyautar daga cikin albashinsa, domin nuna jin daɗinsa ga yadda gwamnan ke ƙoƙarin haɓaka fannin ilimi a jihar.

A cewarsa, matakin malamin na nuna goyon baya da amincewa da manufofin gwamnatin jihar wajen inganta ilimi da walwalar al’umma.

Rahoton ya nuna cewa wannan kyauta na daga cikin misalan yadda wasu ‘yan ƙasa ke nuna jin daɗinsu ga ayyukan gwamnati a fannin ilimi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button