Labarai

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa kaptin ɗin kungiyar Super Eagles, Ahmed Musa a matsayin sabon shugaban gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars.

Cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce naɗin wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa ƙungiyar gabanin fara sabuwar kakar Premier Najeriya.

Dawakin Tofa ya ce an naɗa Ahmed Musa – wanda ɗan wasan ƙungiyar ne – bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki a harkokin wasanni a faɗin jihar.

A watan Octoban 2024 ne Kano Pillars ta sanar da ɗaukar kyaftin ɗin na Najeriya, Ahmed Musa domin buga mata wasanni Premier Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button