Siyasa

An bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Zabi Kabiru Alasan Rurum a Matsayin Mataimakinsa’ a 2027

Wannan kira na kunshe ne cikin wani sako da wasu magoya baya suka fitar, inda suka bayyana cewa ba Rurum ne ke neman mukamin ba, sai dai al’umma da masu kishin jihar Kano ne ke nuna sha’awar ganin ya rike wannan matsayi, bisa la’akari da kwarewarsa da tasirinsa a siyasar jihar.

Magoya bayan sun jaddada cewa Rurum na da karfin fada a ji musamman a yankin Kano ta Kudu, tare da tarihin ayyukan raya kasa a mazabunsa.

 

Sun kuma tuna rawar da ya taka a lokacin da yake rike da mukamin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, inda suka ce ya nuna kwarewa wajen warware matsalolin siyasa masu sarkakiya.

 

A cewarsu, bai wa Rurum wannan dama zai taimaka wajen hada kan jam’iyyar APC a Kano, da kuma bai wa matasa da sauran ‘yan yankin damar samun guraben aiki da mukamai bisa cancanta.

 

Haka kuma, sun bayyana cewa Rurum na da kyakkyawar alaka da ‘yan siyasa a matakin jiha da na kasa, wanda hakan zai taimaka wajen karfafa jam’iyya da kuma samun nasara a zaben 2027.

 

Daga karshe, an bukaci Rurum da ya amince da wannan kira idan aka bukace shi, domin ci gaban jihar Kano baki daya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button