Ketare

Jam’iyyar NRM mai mulki a Uganda ta ayyana shugaban ƙasar, Yoweri Museveni a matsayin wanda zai yi mata takara a zaɓe mai zuwa.

Matakin zai bai wa shugaban ƙasar – wanda ya fi kowa jimawa kan mulkin ƙasar – damar tsawaita kusan shekara 40 da ya shafe yana jagorantar ƙasar.

A jawabin amincewa da takarar da ya yi, Mista Museveni ya ce idan ya yi nasara a zaɓen zai samu damar cimma muradinsa na mayar da ƙasar ”cikin jerin ƙasashen masu masu tasowa”.

Masu sukar shugaban, sun zarge shi da mulkin kama karya tun bayan da ya ƙwace mulkin ƙasar a matsayin jagoran ƴantawaye a 1986.

Tun daga lokacin ne ya riƙa lashe duka zaɓukan ƙasar da aka gudanar, yayin da aka yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima har sau biyu, domin cire ka’idar shekaru da wa’adi domin ba shi damar ci gaba da zama a kan karagar mulki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button