Labarai

Sama da mutane 15 sun kwanta dama asakamakon wani mummunan hari da lakurawa suka kai jihar sokoto

Rahotanni na bayyana cewa wasu da ake zargin mambobin ƙungiyar Lakurawa ne sun hallaka akalla mutane 15 a wani mummunan hari da suka kai ƙauyen Kwalajiya da ke ƙaramar hukumar Tangaza.

Majiyar jaridar Daily Trust ta bayyana cewa harin na iya zama martani da mambobin ƙungiyar suka mayar bayan da wasu daga cikin mayaƙan su suka rasu lokacin da suka kai wani harin da basu samu nasara ba.

Wani shugaban al’ummar yankin da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce, suna cikin masallaci lokacin da aka kawo harin, sannan mayaƙan sun fara harbe-harbe ba bata lokaci.

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro da shugaban ƙaramar hukumar Tangaza sun ziyarci ƙauyen a ranar Laraba domin halartar jana’izar waɗanda suka rasa rayukansu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button