Labarai

Wata Kungiya mai zaman kanta ta bayyana rashin jin daɗinta kan rahoton da ta fitar dangane da kisan mutane biyar da ya faru a jihar Kano

A wata sanarwa da jami’in kungiyar a Kano, Saed Adam Mohammed, ya sanya wa hannu ranar 7 ga Mayu, 2026, kungiyar ta ce Amnesty International ta yi gaggawar alakanta lamarin da siyasa ba tare da cikakken binciken adalci da gaskiya ba.

 

 

Kungiyar ta bayyana cewa, bisa bayanan da suke samu daga yankin, rikicin da ya faru ranar Talata 5 ga Mayu, 2026, fada ne tsakanin wasu kungiyoyin bata-gari da suka dade suna rikici da juna, ba tare da wata hujja da ke danganta gwamnatin jihar Kano ko jami’an siyasa da lamarin ba.

 

 

Sanarwar ta kuma nuna damuwa kan yadda Amnesty International ta dogara da bidiyoyi da suka yadu a kafafen sada zumunta da kuma bayanan da ba a tabbatar da su ba wajen yin zarge-zarge masu nauyi da ka iya tayar da hankula tare da bata sunan jihar Kano a idon duniya.

 

 

Kungiyar ta ce abin takaici ne yadda ake kokarin bayyana rikicin a matsayin siyasar daba ba tare da cikakkun hujjoji ba, lamarin da ka iya bata sunan mutane da hukumomi marasa laifi.

 

 

Haka kuma kungiyar ta yabawa gwamnatin Abba Kabir Yusuf kan matakan da take dauka wajen dakile matsalar daba da tashin hankalin matasa, inda ta yi nuni da shirin “Safe Corridor” da aka amince da shi domin gyaran halayen matasa masu neman tuba.

 

 

Daga karshe, kungiyar ta bukaci hukumomin da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike mai gaskiya domin gano masu hannu a lamarin tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi bisa doka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button