Ƙungiyar Karuwai a Najeriya Ta Yi Kira ga Tinubu, Ta Nemi Kariya Daga Cin Zarafi, Cin Mutunci da Karɓar Kuɗi da Tilastawa daga Abokan Hulɗa da Jami’an Tsaro.
A ƙarƙashin dokar Najeriya, karɓar kuɗi da Tilastawa daga wani jami’in gwamnati ko wani mutum dabam, laifi ne daga cikin kundin laifuffuka, ba tare da la’akari da irin aikin da wanda aka yi wa laifin yake yi ba.

Ƙungiyar Karuwai a Najeriya Ta Yi Kira ga Tinubu, Ta Nemi Kariya Daga Cin Zarafi, Cin Mutunci da Karɓar Kuɗi da Tilastawa daga Abokan Hulɗa da Jami’an Tsaro.
Ƙungiyar ta (NSWA) ta yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta ɗauki matakan gaggawa domin kare Karuwai a faɗin ƙasar daga cin zarafi, tashin hankali, cin mutunci da karɓar kuɗi da Tilastawa.
Mai Gudanarwa na Ƙasa, Amaka Enemo, ta yi wannan kira ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a Legas a ranar Talata, inda ta yi nuni da rahotannin baya-bayan nan da ke nuna ƙaruwar hare-haren jiki, cin zarafi da kuma karɓar kuɗi da Tilastawa da ake yi wa mata masu zaman kansu daga abokan hulɗarsu da kuma wasu jami’an tsaro.
Enemo ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro da su amince da haƙƙoƙi da mutuncin ma’aikatan jima’i, tare da tabbatar da kariyarsu daga tashin hankali da cin zarafi.
Ta jaddada cewa ya kamata a ɗauke su a matsayin mutane masu haƙƙin samun muhimman haƙƙoƙin ɗan Adam da kariya, ba a matsayin masu aikata laifuka ba.
Ta bayyana cewa Karuwai a Nigeria suna fuskantar tashin hankali na tsana, wariya da tozarta su, duk da muhimmiyar rawar da suke takawa a cikin tattalin arziki da al’umma.
Ta ce irin wannan tashin hankali yana jefa rayukansu cikin haɗari tare da tauye haƙƙoƙinsu da mutuncinsu.
Ta jaddada cewa samun tsaro da ’yanci daga tsoro na daga cikin muhimman haƙƙoƙin da ya kamata mutum ya samu, sannan ta yi kira da a ƙara amincewa da haƙƙoƙin mata masu zaman kansu tare da girmama su.
’Yan Sandan Anambra Sun Kama Wata Mace Kan Zargin Cin Zarafin Yaro Ta Hanyar Jima’i Bayan Wani Bidiyo Da Ya Yadu Ya Nuna Ta Tana Amfani da Kayan Jima’i kan Ƙaramin Yaro.
Enemo ta danganta tsaron karuwai da jin daɗinsu zai hana afkuwar laifuka makamantan waɗancan sannan ta kuma alakanta lamarin da manyan batutuwan da suka shafi lafiyar jama’a, inda ta bayyana cewa ƙarfafa kariya na iya taimakawa wajen rage yaɗuwar cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima’i, ciki har da HIV.
Ta roƙi hukumomin tabbatar da doka, da su tabbatar da cewa jami’ansu suna gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa yayin mu’amala da mata masu zaman kansu a maimakon cin zarafi.
Ƙungiyar ta gabatar da shawarar a samar da cikakken horo ga jami’an tabbatar da doka, akan hanyoyin tsaro na bayar da rahoton cin zarafi, da kuma ɗaukar alhaki kan jami’an da aka samu da alhakin tashin hankali ko nuna wariya.
Haka kuma ta yi kira da a gudanar da kamfen na wayar da kan jama’a domin rage kyama da tozarta Karuwai, tare da gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifuka, da kuma tabbatar da cewa waɗanda aka zalunta suna samun damar neman adalci.
Enemo ta bayyana cewa NSWA za ta ci gaba da fafutukar kare haƙƙoƙi, mutunci da tsaron mata masu zaman kansu a faɗin Najeriya.
Ta yi kira ga hukumomin gwamnati, ƙungiyoyi masu zaman kansu da jama’a da su haɗa kai da ƙungiyar domin magance rashin adalci da tauye mutuncin mambobinta.
SOURCE; The Metro Lawyer




