Labarai

Sagama Homes da DanMama Smart Homes Sun Kulla Yarjejeniyar Gina Gidaje a Najeriya

Kamfanin Sagama Homes Ltd. da DanMama Smart Homes Ltd. sun kulla yarjejeniyar haɗin gwiwa domin inganta harkar samar da gidaje na zamani a Najeriya.

 

 

Shugaban Sagama Homes, Ali Nuhu, ne ya kai ziyarar aiki zuwa hedikwatar kamfanin DanMama Smart Homes, inda ya samu rakiyar Babban Manajan kamfanin, Alhaji Salihu Aliyu Maitasamu.

 

 

A yayin ziyarar, sun gana da Shugaban Kamfanin DanMama Smart Homes, Saleem Ilyasu Goje, tare da tawagarsa, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi haɗin gwiwa wajen bunƙasa harkar gidaje.

 

 

Sanarwar da Salisu Mahmud Kura ya fitar a madadin Sagama Homes ta bayyana cewa bangarorin biyu sun mayar da hankali kan yadda za su haɗa ƙarfi da ƙwarewa domin samar da ingantattun ayyuka ga al’umma, musamman a fannin gine-ginen zamani.

 

 

Da yake jawabi, shugaban Sagama Homes ya jaddada kudurinsa na yin aiki tare da abokan hulɗa domin kawo ci gaba a masana’antar gidaje, yana mai cewa haɗin kai shi ne ginshiƙin samun nasara.

 

 

A nasa ɓangaren, kamfanin DanMama Smart Homes ya bayyana farin cikinsa da wannan haɗin gwiwa, yana mai cewa zai buɗe sabbin hanyoyi da fasahohi da za su amfani al’umma.

 

 

Ana sa ran wannan haɗin gwiwa zai samar da damarmaki masu yawa ga ‘yan Najeriya wajen mallakar gidaje cikin sauƙi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button