Ketare
Tawagar wakilan Amurka ta nufi Pakistan don tattaunawa da Iran

Mun samu sabbin bayanai daga Shugaban Amurka, Donald Trump game da batun tattaunawar tsagaita wuta da Iran.
“Wakilaina za su tafi birnin Islamabad na Pakistan – Za su isa can gobe da maraice, domin tattauanawa”, kamar yadda ya rubuta a shafinsa na sada zumunta.
”Muna son cimma yarjejeniya mai kyau kuma mai inganci, kuma ina fata Iran za ta amince da hakan, domin idan ba ta amince ba, Amurka za ta kai hari kan kowace cibiyar lantarkin da duka gadojin Iran,” kamar yadda ya wallafa.
Ya yi gargaɗin cewa ”babu wata lallaɓa da za a yi mana”, idan aka gaza cimma matsaya.
Shugaban na Amurka ya ce zai ruguza duka gadoji da tasoshin lantarki cikin ”hanzari, kuma cikin sauƙi”.




