Dalilin da yasa Kwankwaso ya fuche daga jam’iyyar NNPP

Jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar bayan shafe kusan shekaru huɗu yana cikinta.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da manyan jiga-jigan adawar Najeriya ke ƙoƙarin ƙulla wani ƙawancen siyasa domin tunkarar jam’iyya mai mulki a zaɓen 2027.
Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne sakamakon halin da siyasar ƙasar ke ciki, inda ya ce akwai buƙatar haɗin kai domin kawo sauyi nagaria
A cewarsa, “matakin ya zama tilas domin haɗa kai da wata jam’iyya da za ta ba ni damar kawo sauyi ga ƙasarmu.”
Ya kuma gode wa magoya bayansa da shugabannin jam’iyyar daga matakin mazaɓa zuwa na ƙasa bisa goyon bayan da suka ba shi a tsawon zamansa a NNPP.
Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 a ƙarƙashin NNPP, ya shiga jam’iyyar ne a 2022, inda ya samu nasarar kafa gwamnati a Kano bayan jam’iyyarsa ta lashe zaɓen gwamna.




