Siyasa
Kotu Ta Yi Watsi da Bukatar Dakatar da Tsige Mataimakin Gwamnan Kano

Babbar Kotun Tarayya ta ƙi amincewa da bukatar da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, domin dakatar da Majalisar Dokokin Jihar Kano daga yunkurin tsige shi.
Mai shari’a S M Shaibu ne ya yanke wannan hukunci, inda ya bayyana cewa mai karar bai cika sharudan da ake bukata ba domin a ba shi wannan umarni na wucin gadi.
Kotun ta kuma umurci Mataimakin Gwamnan da ya mikawa wadanda ake kara takardun kotu, domin su samu damar mayar da martani kan karar.
A wani bangare kuma, an ruwaito cewa a ranar 11 ga Maris 2026, kotu ta bayar da wani umarni da ya hana Mataimakin Gwamnan daukar duk wani mataki da zai kawo cikas ga Majalisar Dokokin Jihar Kano wajen gudanar da ayyukanta bisa kundin tsarin mulki.



