An Nada Sabon ko’odineta a jihar Gombe a Shirin “Obi For Nigeria 2027”

Kungiyar “Obi For Nigeria 2027” ta sanar da nadin Malam Khaleed Yahaya Salahudden a matsayin sabon ko’odineta na Gombe domin jagorantar ayyukan yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a zaben 2027, Peter Obi.
A cikin wata takardar nadin da kungiyar ta fitar, ta bayyana cewa an ba Salahudden wannan mukami ne bisa la’akari da manufar kungiyar ta “hadin kai babu bambance-bambance” domin samar da ingantacciyar Najeriya.
Takardar ta nuna cewa sabon ko’odinetan zai jagoranci shirye-shiryen kafa shugabannin jiha, kananan hukumomi da kuma matakin mazabu, tare da tabbatar da cikakken tsari na shugabanci kamar yadda kundin tsarin kungiyar ya tanada.
Haka kuma, an dorawa Salahudden alhakin tabbatar da cewa dukkan shugabannin kungiyar a matakai daban-daban sun cika bayanansu yadda ya kamata, tare da mikawa hedikwatar kungiyar domin adanawa.
Bugu da kari, an umurce shi da tabbatar da cewa dukkan mambobin shugabanci na kungiyar sun kasance ‘yan jam’iyyar ADC tare da tantance katin shaidar mambobinsu.
Kungiyar ta kuma bukaci sabon ko’odinetan ya jagoranci yakin wayar da kai da tallata manufofin “Obi For Nigeria 2027” a fadin jihar Gombe, tare da shirya taruka da gangamin siyasa idan aka samu amincewar hedikwata.
Salahudden zai kuma rika mika rahotannin ayyukan da aka gudanar a matakin jiha, kananan hukumomi da mazabu, baya ga nadin shugabanni a matakai daban-daban domin karfafa tsarin kungiyar.
A wani bangare, an bayyana cewa zai kasance cikin masu sa ido a rumfunan zabe domin kare kuri’u da tabbatar da sahihancin sakamakon zabe, tare da aikawa hedikwata kwafe na sakamakon zaben.
Kungiyar “Obi For Nigeria 2027” ta bayyana godiyarta ga Salahudden bisa amincewarsa da wannan aiki tana mai jaddada cewa za a gane kokarinsa idan aka cimma burin nasarar dan takararta a zaben 2027.




