Gwamnatin Kano Ta Karyata Zargin Raina Sarkin Kano a Hawan Nasarawa

Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da rahotannin da ke yawo a wasu kafafen sada zumunta da ke zargin Gwamna Abba Kabir Yusuf da raina ko watsi da Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, yayin Hawan Nasarawa da aka gudanar a Fadar Gwamnati, tana mai cewa zarge-zargen ba su da tushe balle makama.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin, gwamnatin ta bayyana zargin a matsayin ƙarya tsagwaronta da aka kirkira domin yaudarar jama’a da kuma haddasa rikici a tsakanin al’umma.
Sanarwar ta ce tun kafin gudanar da Hawan, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da Sarkin Kano halin da ake ciki, tare da umartar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano da wasu manyan jami’an gwamnati su karɓi Sarkin a madadinsa a Fadar Gwamnati.
Har ila yau, gwamnatin ta bayyana cewa gwamnan ya halarci Sallar Idi karkashin jagorancin Sarkin Kano, sannan ya kuma halarci Hawan Daushe a masarautar Gaya, tare da shirin karɓar sarakunan Rano, Karaye da Gaya da kansa.
Gwamnatin ta ƙara da cewa, bisa al’adar da aka saba, gwamnonin jihohi kan halarci gaisuwar Sallah tare da Shugaban Ƙasa, inda ta ce a bana bikin Eid-el-Fitr ya zo daidai da wani muhimmin taron shekara-shekara na gwamnonin Najeriya, lamarin da ya sa jadawalin gwamnan ya cika.
A ƙarshe, gwamnatin ta buƙaci al’umma da su yi watsi da rahotannin marasa tushe, tare da jaddada muhimmancin dogaro da sahihan bayanai daga hanyoyin hukuma.




