Labarai

Gidauniyar Baitulkhair Ta Tallafa Wa Marasa Lafiya Da Masu Karamin Karfi ‘A jihar Kano

Gidauniyar Baitulkhair Charity Foundation, karkashin jagorancin Hajiya Halimatu Abdullahi, ta ci gaba da ayyukan alheri na tallafa wa al’umma, inda ta ziyarci Asibitin Marmara da ke yankin Karamar Hukumar Birni domin rabon tallafin kudi ga marasa lafiya da ke kwance a asibitin.

 

Sama da mutane 50 ne suka amfana da wannan tallafin da suka futo daga sassa daban daban-daban na kano

 

Da take karin haske ga manema labarai yayin rabon tallafin, Hajiya Halimatu Abdullahi ta bayyana cewa wannan ba shi ne karon farko da gidauniyar ke gudanar da irin wannan aikin ba.

 

Ta ce tun a lokacin azumin watan Ramadan da ya gabata, gidauniyar ta kai kayan abinci gidajen gyaran hali da asibitoci, tare da rabawa masu karamin karfi domin rage musu radadin rayuwa.

 

 

Shugabar gidauniyar ta kuma kara da cewa nan gaba, gidauniyar za ta maida hankali kan mata masu aikata abin da bai dace ba.

 

 

Manufar ita ce a yi musu nasiha tare da basu jari domin su dogara da kansu, su zama mutane nagari a cikin al’umma.

 

 

Wannan mataki na nuna jajircewar gidauniyar wajen inganta rayuwar al’umma ta fuskoki daban-daban.

 

 

Gidauniyar Baitulkhair ta yi fice wajen gudanar da ayyukan jin kai, wanda hakan ke nuna irin kokarin da take yi wajen ciyar da al’umma gaba da kuma samar da zaman lafiya ta hanyar tallafa wa mabukata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button