Labarai

Dagacin Yankusa Ya Gargadi Matasa Kan Shigar Banza a lokutan bukukuwan Sallah,

Dagacin garin Yankusa da ke ƙaramar hukumar Kumbotso, Malam Bala Isa, ya gargadi matasa maza da mata da su guji shigar banza da askin banza yayin bukukuwan Sallah.

 

 

Ya bayyana cewa irin waɗannan halaye ba su dace da tarbiyya da al’adun Musulunci ba, musamman a lokacin da ake gudanar da bukukuwa masu muhimmanci kamar Sallah.

 

 

Haka kuma, Dagacin ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da amfani da darussan da suka koya a watan Ramadan, tare da tabbatar da cewa sun riƙe kyawawan halaye da ibadu da suka saba yi a lokacin azumin.

 

 

Malam Bala Isa ya kuma jaddada muhimmancin taimakon juna, inda ya bukaci mawadata da su ƙara ƙaimi wajen tallafawa marasa ƙarfi da kuma kula da marayu domin rage radadin rayuwa a tsakanin al’umma.

 

 

Bugu da ƙari, ya shawarci matasa da su zama jakadu nagari a cikin al’umma, tare da yin koyi da abubuwan alheri da suka amfana da su daga darussan tafsiri da aka gabatar a watan Ramadan.

 

 

A ƙarshe, Dagacin ya sanar da cewa za a gudanar da sallar Idi a Babban Masallacin Idi na garin Yankusa da misalin ƙarfe 8:30 na safe.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button