KAROTA Ta Tura Ma’aikata 1,000 Domin kula da Zirga-Zirgar ababan hawa a Lokacin bikin Sallah

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar Kano, Kano Road Traffic Agency, ta sanar da tura ma’aikata 1,000 a wurare masu muhimmanci domin tabbatar da tsaro da sauƙaƙe zirga-zirga yayin bukukuwan Eid al-Fitr da ke tafe.
A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce an ɗauki matakin ne domin tabbatar da kwanciyar hankali da kuma rage cunkoson ababen hawa a lokacin bukukuwan.
Rahotanni sun nuna cewa za a girke jami’an ne a muhimman wurare kamar filayen Sallar Idi, manyan tituna da kuma wuraren shakatawa da ake sa ran jama’a za su taru da yawa.
Manajan Daraktan KAROTA, Faisal Mahmud Kabir, ya bayyana cewa hukumar na ci gaba da jajircewa wajen kare lafiyar masu amfani da hanya da kuma tabbatar da zirga-zirga cikin tsari a lokacin bukukuwan.
Ya kuma bukaci direbobi da su bai wa jami’an zirga-zirga hadin kai tare da bin dokokin hanya domin kauce wa hatsurra da cunkoso.
Haka zalika, shugaban sashen ayyuka na hukumar, Auwal Shehu Muhammad Kofar Mata, ya ce hukumar na yi wa daukacin al’ummar jihar fatan gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali da tsaro.
Sanarwar ta fito ne ta hannun jami’in hulda da jama’a na KAROTA, Abubakar Ibrahim Sharada.




