Rundunar tsaron Civil Defence Ta Cafke Mutane 6 Kan Lalata Digar Jirgin Ƙasa a Kano

Rundunar tsaron Civil Defence a Jihar Kano ta cafke wasu mutane shida da ake zargi da lalata ƙarfen digar jirgin ƙasa a Ƙaramar Hukumar Kiru.
Kwamandan rundunar a jihar, Mohammed Hassan Agalama, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Laraba, 18 ga Maris, 2026.
Ya ce jami’an rundunar sun kama Sulaiman Salisu mai shekaru 45, Musa Aliyu Harisu mai shekaru 22, Ishaq Alhassan mai shekaru 20, Isa Aminu mai shekaru 35, Sadiq Bala mai shekaru 20 da Mansur Idris mai shekaru 22, inda ya bayyana cewa dukkansu ’yan asalin Jihar Kaduna ne.
A cewar kwamandan, an cafke wadanda ake zargin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma gudanar da sintiri, inda aka same su suna aikata laifin lalata ƙarfen digar jirgin ƙasa.
Ya kara da cewa rundunar ta kuma kwato wasu sassa na kayan aikin jirgin ƙasa da kuma kayan da ake zargin suna amfani da su wajen aikata wannan laifi.
Rundunar ta tabbatar da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.




