Rundunar Civil Defence Ta Tura Jami’ai Sama da 3,400 Domin Tabbatar da Tsaro a Kano Lokacin Bukukuwan Sallah

Rundunar Civil Defence Corps (NSCDC) reshen Jihar Kano ta sanar da tura jami’anta sama da 3,400 a sassa daban-daban na jihar domin tabbatar da tsaro kafin, lokacin, da kuma bayan bukukuwan Eid-el-Fitr.
Kwamandan rundunar a jihar, Hassan Mohammed Agalama, ne ya bayyana hakan, inda ya ce matakin na daga cikin shirye-shiryen da rundunar ta dauka domin kare muhimman kadarorin gwamnati da kuma tabbatar da zaman lafiya yayin bukukuwan Sallah a fadin jihar.
A cewarsa, an jibge jami’an tsaro a wuraren gudanar da sallar Idi, wuraren shakatawa, kasuwanni, tashoshin mota da sauran wuraren da jama’a ke yawan taruwa domin hana duk wata barazanar tsaro.
Ya kuma kara da cewa rundunar ta mayar da hankali wajen kare muhimman kayayyakin more rayuwa kamar na wutar lantarki, ruwan sha, hasumiyoyin sadarwa da sauran kadarorin gwamnati.
Kwamandan ya bayyana cewa an kara karfafa bangaren tattara bayanan sirri da sintiri, yayin da aka tanadi tawagogin gaggawa domin daukar mataki cikin sauri idan bukatar hakan ta taso.
Haka kuma, rundunar ta jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da doka da oda a lokacin bukukuwan Sallah.
NSCDC ta kuma bukaci al’ummar jihar da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani motsi ko abu da ake zargi ga hukumomin tsaro mafi kusa. An kuma shawarci iyaye da masu kula da yara da su ja hankalin yaransu kada su shiga ayyukan da suka saba wa doka.
A karshe, kwamandan ya tabbatar wa da al’ummar Jihar Kano kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi, tare da kira ga jama’a da su gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana da bin doka.
Sanarwar ta fito ne ta hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar a jihar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, a madadin kwamandan rundunar.



