Malam Mu’azu Ibni Muhammad Ya Gargadi Musulmi Kan Sukan Iran Da Fifita Kasashen Yahudawa

Shugaban makarantar Shashimatul Islam Bidarasatul Islam, Malam Mu’azu Ibni Muhammad Ibni Abubakar Ibni Sulaiman, ya jaddada muhimmancin neman ilimi ga dukkanin al’ummar Musulmi, yana mai cewa a wannan zamani ilimi ya zama wajibi domin cigaban al’umma.
Malam Mu’azu ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da wakilin Ahrasjo News a wajen rufe karatun tafsirin watan azumin Ramadan da yake gabatarwa a kowace shekara.
Ya ce a halin yanzu akwai alamun da ke nuna cewa ana kokarin maida ilimi baya a wasu wurare, lamarin da ya ce ya kamata al’ummar Musulmi su tashi tsaye domin kare martabar ilimi da kuma bunkasa shi.
“Yau ilimi ya zama wajibi ga kowane Musulmi, domin shi ne ginshikin cigaban rayuwa da kuma fahimtar addini yadda ya kamata,” in ji shi.
Har ila yau, Malamin ya yi kakkausan jan kunne ga wasu daga cikin al’umma kan kalaman da ake furtawa game da Iran, yana mai cewa bai dace Musulmi su rika fifita kasashen Yahudawa a kan kasashen Musulmi ba saboda sabanin fahimta ko akida.
Ya kara da cewa duk da bambancin fahimta da ke tsakanin Musulmi, wajibi ne a rika kiyaye mutuncin juna tare da kauce wa kalaman da ka iya haifar da rarrabuwar kawuna a cikin al’umma.
Malam Mu’azu ya kuma bukaci matasa da sauran al’ummar Musulmi da su dage wajen neman ilimin addini da na zamani domin gina al’umma mai nagarta da fahimta.




