Haɗarin Jirgin Ƙasa Ya Jikkata Fasinjoji A Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Wani jirgin ƙasan fasinja da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ya yi haɗari a safiyar Litinin, lamarin da ya jikkata mutane da dama tare da jefa fasinjoji cikin firgici.
Rahotanni daga Kaduna sun ce haɗarin ya faru ne bayan an ƙara wani tarago ga jirgin a yankin Jere kafin tafiyar ta yi nisa.
Wasu daga cikin fasinjojin da lamarin ya rutsa da su sun bayyana cewa jirgin ya taso daga Kaduna da misalin ƙarfe 7:15 na safiya, amma daga bisani taragon da aka ƙara ya kwance daga jirgin, abin da ya haddasa haɗarin.
Bayanai sun nuna cewa an ɗauki ɗan lokaci kafin a gyara jirgin domin ci gaba da tafiya zuwa Abuja
Shaidun gani da ido sun ce fasinjoji da dama sun shiga cikin firgici da gajiya sakamakon tsoron abin da ya faru.
Hanyar jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja na daga cikin hanyoyin sufuri da dubban matafiya ke amfani da su a kullum, duk da cewa a lokuta da dama ana samun rahotannin irin waɗannan haɗura a kan layin jirgin.
Hikima Radio




