Ketare

Gobara a Asibitin Indiya Ta Hallaka Marasa Lafiya 10

Aƙalla marasa lafiya 10 ne suka mutu sakamakon gobarar da ta tashi a sashen kula da marasa lafiya masu matsanancin hali (ICU) na wani babban asibiti a gabashin India, kamar yadda jami’ai suka bayyana.

Rahotanni daga New Delhi sun ce gobarar ta tashi ne a sashen kula da masu raunuka na SCB Medical College and Hospital da ke birnin Cuttack a jihar Odisha da misalin karfe 2:30 na safiyar Litinin agogon wurin.

Jami’ai sun ce a lokacin da gobarar ta tashi, akalla marasa lafiya 23 na kwance a sashen ICU, inda 10 daga cikinsu suka rasu yayin da ake kokarin kwashe su zuwa wuri mafi aminci domin tsira daga gobarar.

Gwamnan jihar Mohan Charan Majhi ya bayyana cewa ana zargin wata matsalar lantarki ce ta haddasa gobarar a cibiyar kula da masu raunuka a farkon safiyar Litinin.

A cewarsa, dukkan wadanda suka mutu marasa lafiya ne da ke jinya a asibitin, yayin da ma’aikatan asibiti 11 suka samu raunukan konewa yayin kokarin ceton marasa lafiyar daga gobarar.

“Ma’aikatan lafiya da jami’an tsaro sun yi barazanar rayukansu wajen ceton marasa lafiyar, kuma a yayin hakan su ma sun samu raunuka,” in ji gwamnan.

Jami’an kashe gobara sun yi gaggawar zuwa wurin lamarin inda suka samu nasarar shawo kan gobarar, sannan aka kwashe sauran marasa lafiya zuwa wasu sassa na asibitin domin ci gaba da kula da su.

SCB Medical College and Hospital na daga cikin manyan asibitocin gwamnati a jihar Odisha.

Gwamnatin jihar ta sanar da bayar da tallafin kudi ga iyalan wadanda suka mutu, yayin da gwamna Mohan Charan Majhi ya umarci a gudanar da binciken shari’a kan lamarin tare da daukar mataki mai tsauri kan duk wanda aka samu da hannu a faruwar gobarar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button