Jama’a na jiran matsayar ’yan sanda kan hawan Sallah a Kano

Al’ummar Jihar Kano na ci gaba da jiran matsayar rundunar ’yan sandan jihar kan ko za a ba da damar gudanar da hawan Sallah na bana ko kuma a dakatar da shi kamar yadda aka yi a shekarun baya.
Hawan Sallah dai bai kasance ana gudanar da shi yadda aka saba ba tun bayan hawar Abba Kabir Yusuf kan karagar mulkin jihar, sakamakon takaddamar masarautar Kano da ta biyo bayan cire Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, tare da mayar da Muhammadu Sanusi II kan karagar sarauta.
Bayan jerin shari’o’i da aka shigar a kotu kan rikicin masarautar, kotu ta bayar da umarnin a ci gaba da kasancewa a inda ake har sai an kammala shari’ar gaba ɗaya.
Wannan umarni ne ya bai wa rundunar ’yan sandan jihar Kano damar dakatar da hawan Sallah a wasu lokuta domin kauce wa yiwuwar tashin hankali.
Sai dai wasu daga cikin al’umma na danganta dakatar da hawan da siyasa da kuma sabanin jam’iyya tsakanin gwamnatin jihar da gwamnatin tarayya a wancan lokaci.
Yanzu kuwa, da gwamnan jihar ya koma jam’iyyar da ke mulki a ƙasa, wasu na ganin akwai yiwuwar a ba da damar gudanar da hawan Sallah, yayin da wasu kuma ke ganin akwai yiwuwar a ci gaba da dakatar da shi har sai an warware takaddamar masarautar gaba ɗaya.
A halin yanzu dai jama’a na ci gaba da jiran sanarwar hukuma daga rundunar ’yan sandan Jihar Kano domin sanin ko za a gudanar da hawan Sallah na bana ko kuwa ba za a yi ba.
A baya dai, yayin wani taron addu’a da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar, Abba Kabir Yusuf ya umarci hakimai da sarakai da su fara shirye-shiryen gudanar da bukukuwan hawan Sallah.




