Iran ta ba jirgin ruwan Turkiyya damar wucewa ta masigar Hormuz

Ministan sufurin kasar Turkiyya, Abdulkadir Uraloğlu, ya ce Iran ta ba wani jirgin ƙasar izinin wucewa ta Mashigar Hormuz.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya ruwaito cewa jirgin yana kusa da ruwan Iran.
Uraloğlu ya ƙara da cewa gwamnati a Ankara ta ɗaga matakin gargaɗi na tsaro zuwa mafi girma dangane da halin da ake ciki a mashigar Hormuz.
Ministan ya ce wasu jirage 14 na ƙasar suna jiran izinin wucewa ta mashigar sannan zai ci gaba da tuntuɓar jami’an Iran kan halin da jiragen ke ciki.
A makon da ya gabata, rundunar juyin juya halin Iran ta bayyana cewa ta karbe iko kan zirga-zirgar ruwa a Mashigar Hormuz a matsayin ramuwar gayya ga hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kasar.
Iran ta kuma yi barazanar kai hari kan kowanne jirgi da ya wuce ta mashigar ba tare da izini ba.
Mojtaba Khamenei, sabon jagoran addinin kasar, ya jaddada a cikin saƙonsa jiya cewa mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a rufe.




