Siyasa

“Za Mu Sa Kafar Wando Ɗaya da Duk Jami’in gwamnatinmu da muka Kama da Yi wa APC Zagon Kasa” – Gwamna Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi zazzafan gargadi ga kwamishinoni da manyan jami’an gwamnatin jihar kan duk wani yunƙuri na cin dunduniyar gwamnati saboda batun sauya sheƙar jam’iyya.

 

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar zaman Majalisar Zartarwar Jihar karo na 38 da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Kano.

 

Ya ce duk wani kwamishina ko babban jami’i da ke kokwanto ko kuma ke ƙoƙarin cin dunduniyar gwamnati saboda komawarta jam’iyyar APC ya kamata ya shirya ajiye aikinsa.

 

A cewarsa, gwamnatinsa ba za ta lamunci jami’in da ke aiki a ƙarƙashin gwamnati amma a lokaci guda yana aiki da wata jam’iyya ta daban ba, domin hakan na iya kawo tangarda ga tafiyar gwamnati.

 

Abba Kabir Yusuf ya ƙara da cewa duk wani jami’i da ke da niyyar sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya ya dace ya ajiye aikinsa domin bai wa gwamnati damar naɗa wanda zai yi aiki da cikakkiyar biyayya.

 

Gwamnan ya kuma buƙaci ‘yan majalisar zartarwar jihar su ci gaba da ba da gudunmawarsu domin tabbatar da nasarar manufofin gwamnatin jam’iyyar APC da kuma ci gaban al’ummar Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button