Labarai

Sarki Aminu Ado Bayero Ya Sanar da ’Yan Sanda Shirinsa na Hawan Sallah

Fadar Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ta sanar da rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano cewa at fara shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Hawan Salla bayan kammala azumin watan Ramadan.

Sanarwar, wadda ta ɗauki kwanan wata 7 ga Maris, 2026, an aike ta ne ga Ibrahim Adamu Bakori, inda fadar ta bayyana cewa hawan sallar za a gudanar da shi daga fadar sarkin da ke unguwar Nassarawa a Kano.

 

Sakataren Sarkin, Abdullahi Haruna Kwaru, ya tabbatar da cewa Sarkin da majalisar masarautar sun amince da shirye-shiryen bukukuwan, waɗanda za su haɗa da hawan Daushe, Nassarawa, da Fanisau.

 

Fadar ta ce an tura wa jami’an tsaro cikakken jadawalin ranakun gudanarwa, lokaci da wuraren da za a yi hawan, tare da nuna godiya ga jami’an tsaro kan haɗin gwiwarsu wajen tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kano.

 

Haka kuma, fadar ta yi addu’a domin samun nasarar gudanar da bukukuwan salla a faɗin jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button